(ABNA24.com) Shaikh Qawuk, ya ce fitowar milyoyin al’ummar kasar ta Iraki don nuna kyammar Amurka, babban sako ne ga gwamnatin Trump.
A jiya ne a birnin Baghdad na kasar Iraki miliyoyin al’umma ne suka fito domin yin tir da kasantuwar sojojin Amurka a kasar Iraki, tare da yin kira da su gaggauta ficewa daga kasar.
Zanga zangar dai ta gudana ne bisa gayyatar da Sayyid Muqtada Sadr ya yi wa Irakawa da su fito cikin lumana domin neman Amurka ta fice daga cikin kasar baki daya.
Tun a ranar 5 ga watan Janairu nan da ake ciki ne dai majalisar dokokin kasar ta Iraki ta fitar da kuduri na yin kira ga Amurka da ta tattara ya nata, ya nata ta bar kasar.
Kiran ya biyo bayan kisan gillan da Amurka ta yi wa Janar Qassim Suleimani na Iran ne, da kuma Injiniya Abu Mahadi al-Muhandis na rundunar sa kai ta Hashdu sha’abi wacce ta murkushe ‘yan ta’addan da suka addabi kasar ta Iraki.
/129